Home » News & Politics » Labaran Talabijin na 13/12/17

Labaran Talabijin na 13/12/17

Written By BBC News Hausa on Wednesday, Dec 13, 2017 | 03:57 PM

 
Kasashen Musulmi sun maida wa Donald Trump murtani, yayin da suka yi kira ga sauran kasashe da su amince da gabacin Birnin Kudus a matsayin babban birnin Falasdinu. Saudiyya da Daular kasashen Larabawa sun sha alwashin bayar da gudunmawar dala miliyan dari, don yaki da ta'addanci a yankin Sahel. Ana kara samun haske game da zamanin cinikin bayi daga Afirka zuwa Amirka, yayin da a Senegal ake aikin gano jiragen ruwan da suka nutse da bayin.