Home » People & Blogs » Dadin Kowa Episode 66

Dadin Kowa Episode 66

Written By AREWA24 on Thursday, Apr 28, 2016 | 09:03 AM

 
ALJANI YA TAKA WUTA . Da sanyin safiya mutanen garin Dadin kowa sun wari gari da fargaba bayan wani mummunan lamari ya faru a makotansu. Yayin da tashin hankalin Furera ya fi na kowa ganin Maigidanta Sallau na kokarin haukacewa tun sa’ar da wani Dan Garuwa yayi masa hadin kwaya. Alawiyya tayi yunkurin komawa wajen Zubby domin ci gaba da aiki, sai dai burinta bai cika ba domin Zubby tayi mata korar kare. Shin me yayi zafi haka ?